An daure wani malamin Islama kan aikata 'ta'addanci'

Uganda Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An dade ana taka takun-saka tsakanin kungiyoyi daban daban na addinin Islama a Uganda

An yanke wa wani malamin addinin Musulunci na Uganda hukunci daurin rai-da-rai, tare da wasu mabiyansa uku saboda aikata ayyukan ta'addanci.

An kuma yanke wa wasu mutum biyu daban hukuncin daurin shekara 30 a gidan yari.

An samu Sheikh Yunus Kamoga da wasu mabiyansa na darikar Tabliq biyar ne da yi wa al'ummar musulmai barazana da jawo rikici a tsakanin sauran malaman addinin, wadanda aka kashe wasu daga cikinsu.

A ranar Litinin ne aka yanke musu hukunci aikata kisan kai.

Ana zargin Sheikh Yunus Kamoga da mabiyansa ne da haddasa wani yanayi na tsoro cikin al'umar Musulmin Uganda.

An same su da laifin aikata ta'addanci ta hanyar kaddamar da zanga-zanga da buga takardu tare da furta kalaman barazana ta lasifika kan sauran malaman addini.

An kashe wasu daga cikin wadanda suka yi wa barazana, kuma masu shari'a uku daga babbar kotun Uganda sun yanke hukuncin cewar, ayyukan mutanen sun taimaka wajen aikata kashe-kashen, duk da cewar an wanke su daga zargin cewar su suka aiwatar da kashe-kashen.

Kashe-kashen da aka yi wa malaman addinin Islama 13 sun razana 'yan Uganda.

'Yan bindiga bisa babur ne suka aikata yawancin kashe-kashen.

An yi kashe-kashen na baya-bayan nan ne a bara inda aka kashe wani malami da dogarinsa a lokacin da suke tafiya a kan wani babban titi.

Hukumomi na fuskantar matsin lambar samo wadanda suka aikata kashe-kashen bayan an wanke Sheikh Kamoga da mabiyansa daga aikata laifukan.

Wasu 'yan Tabliq da ke da irin akidarsa a wajen kotun sun ce gwamnati ne ta kitsa hukuncin da aka yanke wa malamin da mabiyansa, kuma za su daukaka kara domin neman a soke hukuncin.

Amman alkalai sun ce mutanen da aka samu da laifi kuma aka yanke musu hukunci sun gaza saukar da nauyin da ya rataya a kansu a matsayinsu na shugabanni.

Labarai masu alaka