Ba wanda yake son zuwa Anfield wasa - Klopp

"za mu shiga Gasar Zakarun Turai, kuma mun kagu mu samu abokan karawa" Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption "za mu shiga Gasar Zakarun Turai, kuma mun kagu mu samu abokan karawa"

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce ba wanda yake son karawa da kulob din nasu a matakin rukuni na wasannin zakarun Turai saboda yanayin filin wasansu na Anfield.

Ya ce, "za mu shiga Gasar Zakarun Turai, kuma mun kagu mu samu abokan karawa".

Klopp ya kara da cewa, babu wani abu da zai fada game da makomar Philippe Coutinho yayin da rahotonnni ke cewa Barcelona na shirin taya dan wasan a karo na hudu a kan kudi fam miliyan 136.

Labarai masu alaka