Ibrahimovic ya tsawaita zamansa a Man Utd

Zlatan Ibrahimovic ya buga wa United wasa 46 ya kuma ci kwallo 28 a kakar bara. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zlatan Ibrahimovic ya buga wa United wasa 46 ya kuma ci kwallo 28 a kakar bara.

Zlatan Ibrahimovic, ya tsawaita zamansa a Manchester United a kan yarjejeniyar shekara daya.

Tsohon dan kwallon dan kasar Sweden mai shekara 35, ya buga wa United wasa 46 ya kuma ci kwallo 28 a kakar bara.

A watan Yuni ne kulob din ya sake shi, bayan da ya kare kakar ba shiri sakamakon raunin da ya yi a gwiwa, amma ana sa ran zai murmure ya dawo a watan Disamba.

Jose Mourinho ya ce, "Saboda gudunmawar da ya ba mu a kakar bara ya cancanci amincewarmu kuma mu yi hakurin jiran shi ya samu lafiya ya dawo taka-leda".

Labarai masu alaka