Premier: An kashe fam biliyan 1.17 a sayen 'yan wasa

Premier League
Image caption Lukaku ya ci wa United kwallo uku a wasa biyu da ya buga mata gasar Premier

An kashe fam biliyan 1.17 a sayen 'yan wasa a kakar Premier ta bana tun kafin kasuwar ta watse a karshen watan Agustan nan in ji mujallar da ke sharhi kan kasuwanci Deloitee.

Kungiyoyi 20 da ke buga gasar sun kashe kudin ne tun daga lokacin da aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai har zuwa Laraba, wanda ya dara fam biliyan 1.165 da aka biya a bara.

A banar nan Manchester United ta sayi Romelu Lukaku fam miliyan 75 daga Everton, Chelsea kuwa ta dauko Alvaro Morata daga Real Madrid kan fam miliyan 70.

A daidai wannan lokacin a bara kungiyoyin na Premeier sun kashe fam miliyan 865 ne.