Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Turai

UEFA Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karo na uku kenan Ronaldo ya ci kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Turai

Cristiano Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da ya fi yin fice a Turai a shekarar nan a bikin da aka yi a Monaco.

Dan wasan ya doke abokan takararsa da suka hada da Lionel Messi na Barcelona da mai tsaron ragar Juventus, Gianluigi Buffon.

Ronaldo ya taimakawa Real Madrid ta ci kofin Zakarun Turai da aka kammala, kuma na 12 jumulla, inda ya ci kwallo 12 a wasannin.

Nasarar da dan kwallon tawagar Portugal ya yi, ya sa ya lashe kyauta ta uku kenan, ya dara Messi da guda daya.

'Yan wasan Barcelona, Lieke Martens ce ta ci kyautar mata a matakin babu wacce ta kai ta iya taka-leda a Turai a bana.

Ta kuma yi nasara ne a kan 'yar wasan Wolfsburg, Pernille Harder da Dzsenifer Marozsan mai buga tamaula a Lyon.

Labarai masu alaka