Barcelona ta dauki Ousmane Dembele

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dembele ya zama dan wasa na biyu da aka saya mafi tsada a bana a tarihin tamaula a duniya

Kungiyar Barcelona ta amince ta dauki dan kwallon Borussia Dortmund, Ousmane Dembele kan kudin da ake cewa zai kai fam miliyan 135.5.

Hakan ya sa dan kwallon ya zama na biyu mafi tsada a duniya a tarihin tamaula da aka saya a bana, bayan Neymar da ya koma Paris St-Germain kan fam miliyan 200 daga Barcelona.

Barca za ta fara biyan fam miliyan 96.8 daga baya ta cika sauran kudin dan kwallon mai shekara 20, wanda ya amince da yarjejeniyar shekara biyar.

Kungiyar ta Spaniya ta ce ta gindiya fam miliyan 400 ga duk kungiyar da ke son daukar Dembele idan kwantiraginsa bai kare da ita ba.

Dan wasan zai ziyarci Spaniya a ranar Litinin domin likitocin Barcelona su duba lafiyarsa.

Dortmund ba ta sallama tayin da Barca ta fara yi wa dan kwallon a baya ba a watan Agusta, har ma ta dakatar da dan kwallon bayan da ya ki zuwa atisaye.

Labarai masu alaka