Europa League: Arsenal tana rukuni da Cologne

Europa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal za ta kara da Liverpool a wasan mako na uku a gasar Premier

Arsenal tana rukunin da ya kunshi BATE Borisov da Cologne da kuma Red Star ta Belgrade a gasar Europa League da aka raba jadawali a ranar Juma'a.

Wannan ne karon farko a shekara 20 da Gunners, wacce ta yi ta biyar a kan teburin Premier da aka kammala za ta buga gasar ta Europa a bana.

A jawalin da aka raba da ya kunshi kungiyoyi 48, Everton tana rukuni daya da Lyon da Atalanta da kuma Apollon Limassol ta Cyprus.

Za a fara wasannin cikin rukuni a ranar 14 ga watan Satumba:

Ga yadda aka raba kungiyoyin:

Rukunin A: Villarreal, Maccabi Tel Aviv, Astana, Slavia Prague.

Rukunin B: Dynamo Kiev, Young Boys, Partizan Belgrade, Skenderbeu.

Rukunin C: Sporting Braga, Ludogorets, Hoffenheim, Istanbul Basaksehir.

Rukunin D: AC Milan, Austria Vienna , Rijeka, AEK Athens.

Rukunin E: Lyon, Everton, Atalanta, Apollon Limassol.

Rukunin F: FC Copenhagen, Lokomotiv Moscow, Sheriff Tiraspol, FC Zlin.

Rukunin G: Vitoria Plzen, Steaua Bucarest, Hapoel Beer-Sheva, FC Lugano.

Rukunin H: Arsenal, BATE Borisov, Cologne, Red Star Belgrade.

Rukunin I: Salzburg, Marseille, Vitoria Guimaraes, Konyaspor.

Rukunin J: Athletic Bilbao, Hertha Berlin, Zorya Luhansk, Ostersund.

Rukunin K: Lazio, Nice, Zulte Waregem, Vitesse Arnhem.

Rukunin L: Zenit St Petersburg, Real Sociedad, Rosenborg, Vardar.