Liverpool za ta karbi bakuncin Arsenal

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool tana ta shida a kan teburi, ita kuwa Arsenal tana ta 12

Arsenal za ta ziyarci Liverpool domin buga wasan mako na uku a gasar Premier da za su kara a ranar Lahadi a Anfield.

A wasan farko a gasar da Liverpool ta buga ta tashi 3-3 tsakaninta da Watford, sannan ta ci Crystal Palace 1-0.

Ita kuwa Arsenal ta fara da doke Leicester City da ci 4-3, daga nan ta yi rashin nasara a hannun Stoke City da ci 1-0 a wasa na biyu.

A kakar bara da kungiyoyin biyu suka fafata a gasar ta Premier Liverpool ce ta ci Arsenal 4-3 a Emirates, ta kuma doke ta 3-1 a Anfield.