Barcelona ta bai wa Dembele rigar Neymar

Barcelona Hakkin mallakar hoto Marca
Image caption Ousmane Dembele shi ne dan wasa na biyu da aka saya mafi tsada a tarihi a bana

Sabon dan kwallon da Barcelona ta saya mafi tsada a bana, Ousmane Dembele zai saka riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a kungiyar.

Barcelona ta sayi dan wasan ne daga Borussia Dortmund kan kudin da ake cewa zai kai fam miliyan 135.5 domin ya maye gurbin Neymar.

Dan wasan zai isa Spaniya a ranar Lahadi, zai kuma saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar, bayan an duba lafiyarsa, sannan a gabatar da shi a gaban magoya baya da 'yan jarida a ranar Litinin.

Dembele shi ne dan wasa na hudu da Barcelona ta saya a bana da suka hada da Paulinho da Nelson Semedo da kuma Gerard Deulofeu.

A cikin watan Agusta ne Neyma ya koma Paris St Germain kan kudi fam miliyan 200, a matsayin wanda aka saya mafi tsada a tarihi a fagen tamaula a bana.

Neymar ya ci kwallo uku a wasa biyu da ya buga wa PSG a gasar cin kofin Faransa ta bana.