Ko Benzema zai koma Arsenal?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Benzema ya koma Madrid ne a shekarar 2009 daga Lyon

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta iya neman dan wasan gaban Real Madrid Karim Benzema, idan Alexis Sanchez ya bar kungiyar, kamar yadda jaridar Diario Gol ta bayyana.

Tottenham tana zawarcin dan wasan Paris St-Germain (PSG) Serge Aurier a kan fam miliyan 23 gabanin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai, in ji jaridar Guardian.

PSG ta kammala cinikin sayen Kylian Mbappe daga Monaco da kuma dan wasan tsakiya Fabinho, a cewar jaridar Daily Record.

Jaridar sun ta ruwaito cewa ne Chelsea tana tattaunawa da Everton kan batun cinikin Ross Barkley inda ta yi ta ce za ta biya fam miliyan 30.

Kodayake Chelsea tana duba yiwuwar sayen Fernando Llorente na Swansea City, kamar yadda jaridar Daily Telegraph ta wallafa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mustafi mai shekara 25 ya koma Arsenal ne daga Valencia a shekarar 2016

Arsenal za ta sayar da Shkodran Mustafi gabanin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai a ranar Alhamis idan aka samu mai sayensa a kan fam miliyan 35, farashin da suka sayo dan kwallon daga Valencia a bara, in ji jaridar Daily Mail.

Jaridar ta ce Juventus da Inter Milan suna zawarcin dan wasan.

Labarai masu alaka