Premier: Everton za ta ziyarci Chelsea

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Everton tana ta takwas a kan teburin Premier, ita kuwa Chelsea tana ta 11

Kungiyar Chelsea za ta kara da Everton a wasan mako na uku a gasar Premier a ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Chelsea ta sha kashi da ci 3-2 a wurin Burnley a Stamford Bridge a wasan farko a gasar ta Premier, sannan ta ci Tottenham 2-1 a Wembley a wasa na biyu a Wembley.

Ita kuma Everton ta fara cin Stoke City 1-0, sannan ta yi kunnen doki 1-1 da Manchester City, kuma Wayne Rooney ne ya ci mata kwallayen.

A kakar bara a gasar ta Premier Chelsea ta doke Everton da ci 5-0 a Stamford Bridge sannan ta ci ta 3-0 a Goodison Park.

Labarai masu alaka