Barcelona ta hada maki uku a Alaves

La Liga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Messi ya ci kwallo biyu a wasa biyu da ya buga wa Barcelona a La Liga ta bana

Deportivo Alaves ta yi rashin nasara a gida da ci 2-0 hannun Barcelona a wasan mako na biyu a gasar La Liga da suka kara a ranar Asabar.

Barcelona ta ci kwallo ne ta hannun Lionel Messi wanda ya ci ta farko bayan da aka dawo daga hutu a minti na 55 sannan ya kara ta biyu a minti na 66.

Tun farko sai da Messi ya barar da fenariti saura minti shida a tafi hutun rabin lokaci.

Da wannan nasarar, Barcelona wadda ta ci Real Betis 2-0 a wasan farko a Nou Camp ta hada maki shida kenan a karawa biyu a La Ligar bana.

Barcelona za ta karbi bakuncin Espanyol a wasan mako na uku a ranar 9 ga watan Satunba a Nou Camp.