Da kyar Man United ta ci Leicester City

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester United ta ci kwallo 10 a wasa uku, kuma babu kungiyar da ta zura maka kwallo a Premier ta bana

Manchester United ta ci Leicester City 2-0 da kyar a wasan mako na uku a gasar Premier da suka fafata a ranar Lahadi a Old Trafford.

Sai da aka dawo daga hutu ne United ta ci kwallo ta hannun Marcus Rashford da Marouane Fellaini, wadan da suka shiga wasan daga baya.

United ta barar da fenariti ta hannun Remelu Lukaku, inda mai tsaron ragar Leicester City, Kasper Schmeichel ya hana ta shiga raga da sauran hare-hare da United ta dunga kai wa.

Tun farko an yi hasashen cewar United za ta zazzagawa Leicester kwallaye a karawar, ganin a bara a fafatawa ukun da suka yi United ce ta cinye wasannin, daya ma da ci 4-1.

United ta hada maki tara a wasa uku a Premier bana kenan, bayan da ta ci West Ham 4-0 ta kuma doke Swansea ita ma da ci 4-0.

United za ta ziyarci Stoke City a wasan mako na hudu, yayin da Leicester City za ta fafata da Chelsea a Stamford Bridge.

Labarai masu alaka