Damben Shagon Mada da Shamsu Kanin Emi
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Damben Shagon Mada da Shamsu Kanin Emi

Turmi biyu suka taka tsakanin Shagon Mada daga Kudu da Shamsu Kanin Emi daga Arewa kuma babu kisa a safiyar Lahadi a Abuja.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton

Daya daga wasannin da aka dambata a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a safiyar Lahadi a Abuja, Nigeria.

Sauran wasannin da aka yi canjaras aka tashi:

  • Shagon Shagon Dan Kanawa daga Kudu da Shagon Bahagon Sanin Kurna daga Arewa
  • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Shagon Dan Sama'ila daga Kudu
  • Shagon Mai Keffi daga Kudu da Garkuwan Mutanen Karmu daga Arewa
  • Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu da Shagon Garba Dan Malumfashi daga Arewa
  • Dan Hussaini daga Arewa da Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu
  • Aliyun Langa-Langa daga Arewa da Bala Shagon Kwarkwada daga Kudu
  • Dogon Aleka daga Kudu da Shagon Mafarauta daga Arewa
  • Sani Mai Kifi daga Arewa da Dan Daba Shagon Sikido daga Kudu