Guardiola ya bukaci dalilin jan katin Sterling

Man City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester City ce ta ci Bournemouth 2-1 a wasan mako na uku a Premier a ranar Asabar

Koci Pep Guardiola ya bukaci hukumar kwallon Ingila ta yi masa karin bayani kan dalilin da ya sa aka bai wa Raheem Sterling jan kati a karawa da Bournemouth.

Raheem Sterling ne ya ci wa Manchester City kwallo na 2-1 a gasar Premier a ranar Asabar, daga nan ya ruga cikin magoya bayan City domin su taya shi murna.

Nan da nan alkalin wasa, Mike Dean ya daga masa katin gargadi na biyu kuma daman ya yi laifi a baya can, dalilin da ya sa ya ba shi jan kati nan take kenan.

Guardiola ya shaidawa BBC cewar ''Ni bai gane ba, ina fatan za su kirani su yi min bayani kan dalilin da aka ba shi jan katin''.

Gebriel Jesus ne ya fara ci wa City kwallo daga baya Charlie Daniels ya farke wa Bournemouth.

Labarai masu alaka