Chelsea ta ci Everton a ruwan sanyi

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea ta hada maki shida a wasa uku da ta yi a gasar Premier ta bana

Chelsea ta doke Everton da ci 2-0 a wasan mako na uku a gasar Premier da suka kara a Stamford Bridge a ranar Lahadi.

Chelsea ta ci kwallo ta hannun Cesc Fabregas tun kafin aje tuhu, kuma bayan da aka dawo ne ta kara na biyu ta hannun sabon dan wasan da ta saya a bana Alvaro Morata.

Chelsea ce ta mamaye wasan da kaso mafi rinjaye, kuma karawa ta biyu kenan da kungiyar ta yi nasara a gasar ta Premier kakar nan, bayan doke ta da Burnley ta yi a wasan farko.

Kuma Chelsea ta kai hare-hare da dama ta hannun Victor Moses da Pedro a fafatawar.

Wasan hamayya na uku kenan da Everton ta buga a kwana bakwai, kuma ta kasa yin nasara a fafatawa 23 da ta yi a Stamford Bridge kenan.

Chelsea za ta ziyarci Leicester City a wasan mako na hudu a gasar ta Premier, ita kuwa Everton za ta karbi bakuncin Tottenham.

Labarai masu alaka