'Liverpool za ta sayi Chamberlain'

Alex Oxlade-Chamberlain Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Oxalade-Chamberlain ya koma Arsenal ne a shekarar 2011 daga Southampton

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta tashi tsaye kan batun neman Oxlade-Chamberlain, wanda ake ganin ya fi son ya koma Chelsea, kamar yadda jaridar Sunday Mirror ta ruwaito.

Arsenal tana shirin sayen dan kwallon Real Madrid, Marco Asensio, a kan fam miliyan 75 gabanin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai ranar Alhamis, in ji jaridar Sunday Express.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Asensio ya koma Madrid ne daga kungiyar Mallorca a shekarar 2014

Liverpool ta ba Barcelona wa'adin ranar Litinin kan ta fadi kudin da za ta sayi Philippe Coutinho, kamar yadda jaridar Onda Cero ta bayyana.

Everton tana zawarcin dan wasan Leicester City Jamie Vardy a kan fam miliyan 40, sai dai dan wasan ya son komawa Chelsea ne, a cewar jaridar Sunday Mirror.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Vardy mai shakara 30 ya koma Leicester City a shekarar 2012

Arsenal za ta sayar da Kieran Gibbs da Alex Oxlade-Chamberlain da Lucas Perez da Shkodran Mustafi kafin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai, kamar yadda jaridar Sunday Telegraph ta wallafa.

Kungiyar Juventus tana zawarcin dan wasan tsakiyar Barcelona, Andre Gomes, kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai fidda rai kan sayen Thomas Lemar daga Monaco da kuma Virgil van Dijk na Southampton ba, in ji jaridar Sun.

Paris St-Germain ta tashi tsaye kan zawarcin Kylian Mbappe a farashin fam miliyan 166 kafin ranar Alhamis, sai dai Monaco ta fi so ta sayar da dan kwallon ga Real Madrid, kamar yadda Sunday Telegraph ta ce.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mbappe mai shekara 18 ya koma Monaco ne a shekarar 2015

Labarai masu alaka