Liverpool ta lallasa Arsenal da ci 4-0

'Yan wasan Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa takwaranta ta Arsenal da ci 4-0.

Roberto Firmino ne ya fara daga ragar Arsenal minti 17 da fara wasa.

Yayin da Sadio Mane ya kara kwallo ta biyu minti biyar kafin zuwa hutun rabin lokaci.

Sai Mohamed Salah da ci tasa kwallon a minti na 57.

A minti na 77 kuma Daniel Sturridge shi ma ya ci tasa.

Labarai masu alaka