Dortmund ta maye gurbin Dembele da Yarmolenko

Dortmund Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yarmolenko ya koma Dortmund domin ya maye gurbin Dembele

Borrusia Dortmund ta dauki Andriy Yarmolenko kan yarjejeniyar shekara hudu, domin ya maye gurbin Ousmane Dembele wanda ya koma Barcelona da taka-leda.

Yarmolenko mai shekara 27 wanda ya buga wa Dynamo Kyiv wasa 228 daga tsakanin 2008 zuwa 2017 ya ci mata kwallo 99, ya sauka a Signal Iduna Park filin wasa na Dortmund.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Ukraine wanda ya fara buga wa tamaula tun yana da shekara 19, ya yi mata wasa 68 kuma ya ci kwallo 29 kawo yanzu.

Dambele ya koma Barcelona kan fam militan 135.5 a matsayin wanda ta dauka mafi tsada a bana, kuma na biyu da aka saya kudi da yawa bayan Neymar da ya koma PSG daga Barcelona.