Liverpool za ta taya Lemar fam miliyan 60

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Thomas Lemar ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa wasa biyar

Liverpool na shirye-shiryen taya dan kwallon Monaco, Thomas Lemar kan fam miliyan 60 kafin a rufe kasauwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula a ranar Alhamis.

Jorgen Klopp ya dade yana bibiyar wasan Lemar mai shekara 21, amma har yanzu Liverpool ba ta tuntubo Monaco ba kan cinikin dan wasan.

Sayan Lemar da Liverpool ke son yi, bai shafi makomar Philippe Coutinho a Anfield ba.

Liverpool ta ki sallama tayi uku da Barcelona ta yi wa dan kwallon Brazil da kudi ya kai fam miliyan 114.