Liverpool ta sayi Keita mafi tsada a tarihi

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sai a ranar 1 ga watan Yulin 2018 Keita zai koma Anfield da taka-leda

Liverpool ta amince ta sayi dan kwallon Leipzig, Naby Keita a matsayin mafi tsada a kungiyar, amma sai a ranar 1 ga watan Yulin 2018 zai koma Anfield.

Liverpool ta yadda ta biya fam miliyan 48 kudin da Leipzig ta gindaya idan yarjejeniyarsa ba ta kare da kungiyar ba, kuma zai koma Anfield da taka-leda a badi.

Jurgen Klopp ya dade yana zawarcin Keita daya daga cikin 'yan kwallon da ya so ya saya a bana, amma Leipzig ta ki amince wa ya bar Jamus a bana.

Kudin da Liverpool za ta sayi Keita ya dara fam miliyan 35 da kungiyar ta dauko Andy Carroll daga Newcastle United.