Magoya bayan Barca na son shugabanta ya sauka

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A bana ne Real Madrid ta doke Barcelona 5-1 gida da waje a Spanish Super Cup

Bikin gabatar da sabon dan kwallon da Barcelona ta saya, Ousmane Dembele ya ci karo da cikas, bayan da magoya bayan kungiyar suka yi ta rera wakokin neman shugabanta ya yi ritaya.

Dembele mai shekara 20, ya zama na biyu da aka saya mafi tsada a tarihin tamaula a duniya kan fam miliyan 135.5, bayan Neymar wanda ya koma Paris St Germain da murza-leda kan fam miliyan 200.

Bikin ya ci karo da cikas bayan da aka yi jinkirin sa'a biyu, sakamakon rashin samun takardun rijistar dan kwallon daga Dortmund.

A lokacin ne magoya bayan Barcelona 18,000 suka rinka busa usur da rera wakokin cewar Bartomeu ya yi ritaya.

Mahukuntan Barca na shan matsi kan yadda kungiyar ke koma-baya a wasanninta da kuma sayar da Neymar da aka yi zuwa PSG.

Taron bikin bai kai yawan magoya bayan Barcelona 50,000 da suka tarbi Neymar a Nou Camp a shekara hudun da suka wuce ba.

Labarai masu alaka