Ko Dembele zai taka rawar da Neymar ya yi a Barca?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dembele ya koma Barcelona a matsayin na biyu mafi tsada da aka saya a tarihin tamaula

A ranar Litinin Osmane Dembele ya kammala komawa Barcelona daga Borussia Dortmund a matsayin na biyu mafi tsada da aka saya a duniya kan fam miliyan 135.3.

Barcelona ta dauki dan kwallon ne domin ya maye gurbin Neymar wanda ya koma Paris St-Germain kan fam miliyan 200 a matakin wadda aka saya mafi tsada a duniya.

Tuni Barcelona ta bai wa Dembele riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a Barca, shin ko Dembele zai taka rawa irin wacce Neymar ya yi?

Ga jerin kungiyoyin da ya buga wa tamaula da kwallayen da ya ci:

 • Cikakken suna:Ousmane Dembélé
 • Ranar Haihuwa:15 May 1997 (age 20)
 • Wurin da aka haife shi:Vernon, France
 • Tsawonsa:1.78 m (5 ft 10 in)[1]

Taka-leda a matsayin matashin dan kwallo

 • 2004-2009Madeleine Évreux
 • 2009-2010Évreux
 • 2010-2015Rennes

Taka-leda a matsayin kwararren dan wasa

 • 2014-2015Rennes II wasa 22 kwallo 13
 • 2015-2016Rennes wasa 26 kwallo 12
 • 2016-2017Borussia Dortmund wasa 32 kwallo 6

Wasanni a tawagar kwallon Faransa

 • 2013-2014 Tawagar France ta matasa 'yan kasa da shekara 17 wasa 8 kwallo 4
 • 2014-2015 Tawagar France ta matasa 'yan kasa da shekara 18 wasa 5 bai ci kwallo ba
 • 2015 Tawagar France ta matasa 'yan kasa da shekara 19 wasa 3 kwallo 1
 • 2016- Tawagar France ta matasa 'yan kasa da shekara 21 wasa 4 bai ci kwallo ko daya ba
 • 2016- Babbar tawagar France wacce ya yi wa wasa 7 ya ci kwallo 1

Labarai masu alaka