Chelsea na daf da daukar Chamberlain

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta buga wasa uku a Premier ta bana ta ci karawa daya aka doke ta sau biyu

Dan kwallon Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain ya kusa ya koma kungiyar Chelsea mai rike da kofin Premier da taka-leda kan fam miliyan 40.

A karshen kakar badi ne yarjejeniyar Chamberlain mai shekara 24 za ta kare a Emirates, kuma bai saka hannu kan tsawaita zamansa a kungiyar ba.

Oxlade-Chamberlain bai yanke shawarar kungiyar da ya kamata ya koma ba tsakanin Chelsea ko Liverpool, sai dai Chelsea ce kawo yanzu ta taya dan wasan.

Sai dai Arsenal na fatan kammala sayar da tsohon dan kwallon Southampton din ba tare da ba ta lokaci ba.

Dan wasan ya buga wa Arsenal wasannin Premier uku da ta buga a bana, ciki har da karawar da Liverpool ta ci Gunners 4-0 lokacin da aka cire shi a karawar.

Chamberlain zai zama na biyar da Chelsea ta dauka a bana bayan Alvaro Morata da mai tsaron raga Willy Caballero da mai tsaron baya Antonio Rudiger da mai wasan tsakiya Tiemoue Bakayoko.

Labarai masu alaka