Man City na son daukar Sanchez kafin Alhamis

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An ci Arsenal wasa biyu a karawa uku da ta buga a gasar Premier ta bana

Manchester City na son ta sayi dan kwallon Arsenal, Alexis Sanchez kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai a ranar Alhamis.

Sanchez mai shekara 24, ya ci kwallo 24 a Premier bara, sai dai yarjejeniyarsa za ta kare da Arsenal a badi, kuma bai saka hannu kan tsawaita zamansa a Emirates ba.

Kocin Manchester City, Pep Guardiola na son sayen Sanchez kai tsaye kuma ba tare da ba ta lokaci ba.

Sai da kuma idan Sanchez ya koma City, makomar Raheem Sterling za ta zama kila-wa-kala a kungiyar.

Sterling ya buga wa City wasa uku da ta yi a Premier, amma ba a yi masa alkawarin saka shi a wasa akai-akwai ba, sakamakon sayen Bernardo Silva da ta yi daga Monaco.

BBC ta fahimce cewar Sterling zai so ya koma Landan da taka-leda, idan har Arsenal na bukatar hakan a cikin yarjejeniyar cinikin Sanchez.

City ba ta taya Sanchez ba, amma ana sa ran za ta sayi dan kwallon nan ba da dadewa ba.

Labarai masu alaka