Liverpool ta dauki Oxlade-Chamberlain

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chamberlain ya koma Arsenal daga Southampton a 2011

Liverpool ta amince ta dauki dan wasan Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain kan fam miliyan 40.

Dan wasan tawagar Ingila mai shekara 24, ya ki ya koma Chelsea da taka-leda a ranar Talata duk da cewar Arsenal ta amince da tayin da aka yi masa.

Oxlade-Chamberlain ya buga wa Arsenal wasa uku da ta yi a gasar Premier bana, duk da sanar wa da Arsene Wenger cewar ba zai tsawaita zamansa a Gunners ba.

Dan wasan ya buga wa Arsenal tamaula sau 198 tun komawarsa Gunners daga Southampton a watan Agustan 2011.

Kudin da Liverpool ta sayi Chamberlain shi ne na biyu mafi tsada a kungiyar bayan dan kwallon RB Leipzig, Naby Keita da ta dauka kan fam miliyan 48, wanda sai a badi zai koma Anfield.

Labarai masu alaka