Arsenal ta ki sayar wa da City Sanchez

Arsenal
Bayanan hoto,

Arsenal ta yi rashin nasara a wasa biyu daga ukun da ta buga a Premier

Arsenal ta ki sallama tayin fam miliyan 50 da Manchester City ta yi wa Alexis Sanchez domin ya koma Ettihad da murza-leda.

A karshen kakar badi yarjejeniyar Sanchez mai shekara 24 za ta kare da Gunners, kuma yana son ya koma buga tamaula a Manchester City.

Arsenal ba ta yadda da duk wani kokarin da City ke yi na sayen Sanchez ba, kuma tana son Raheem Sterling ya koma Emirates da wasa a cikin cinikin kafin ranar Alhamis.

Shi kuwa kocin Manchester City, Pep Guardiola yana son sayen Sanchez ba tare da bayar da Sterling ba.

Sterling ya buga wa City wasa uku da ta yi a Premier, amma ba a yi masa alkawarin saka shi a wasa akai-akai ba, sakamakon sayen Bernardo Silva da ta yi daga Monaco.