Juventus ta dauki aron Howedes

Juventus Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jamus ce ta lashe kofin duniya a Brazil a 2014, bayan da ta ci Argentina 1-0 a wasan karshe

Dan wasan tawagar kwallon Jamus, mai taka-leda a Schalke, Benedikt Howedes zai buga wa Juventus wasa aro zuwa karshen kakar bana.

Howedes mai shekara 29, ya yi wasanninsa na tamaula tun yana da kuruciya a Schalke, ya kuma yi kyaftin dinta shekara shida.

Juventus ta bai wa Schalke fam miliyan 3.22 domin ya buga mata tamaula, kuma kudin zai kai fam miliyan 11.96 idan ya yi wasa 25 a bana.

Haka kuma Juventus tana da damar sayen dan kwallon idan ya taka rawar gani a kungiyar.

Howedes ya buga wa Jamus wasa 44 har da na gasar cin kofin duniya a 2014 da kasar ta zama zakara a Brazil.

Labarai masu alaka