World Cup 2018: Nigeria za ta kara da Kamaru

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nigeria ce ke mataki na daya a rukuni na biyu da maki shida

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria za ta karbi bakuncin ta Kamaru a ranar Juma'a a wasan shiga gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci.

Super Eagles za ta buga wasan ne ranar 1 ga watan Satumba a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo.

Kwanki uku tsakani ne Super Eagles za ta ziyarci Kamaru a wasa na biyu da za su fafata a Yaounde.

Super Eagles ce ta daya a rukuni na biyu da maki shida bayan da ta yi nasara a kan Zambia da Algeria, Kamaru ce ta biyu da maki biyu wacce ta yi kunnen doki da Algeria ta tashi babu ci da Zambia.

Kocin Kamaru, Hugo Bross ya ce idan har ba su samu maki hudu ba a kan Nigeria a fafatawar da za su yi gida da waje zai yi wahala su halarci Rasha a badi.

Ga wasannin da za a buga a karshen mako:

 • Alhamis: Litinin:
 • Uganda v Egypt (Grp E)Cameroon v Nigeria (Grp B)
 • Guinea v Libya (Grp A)Libya v Guinea (Grp A in Tunisia)
 • Juma'a: Talata:
 • Ghana v Congo (Grp E)Congo v Ghana (Grp E)
 • Nigeria v Cameroon (Grp B)South Africa v Cape Verde (Grp D)
 • Cape Verde v South Africa (Grp D) Ivory Coast v Gabon (Grp C)
 • Morocco v Mali (Grp C)DR Congo v Tunisia (Grp A)
 • Tunisia v DR Congo (Grp A)Burkina Faso v Senegal (Grp D)
 • Asabar:Egypt v Uganda (Grp E)
 • Zambia v Algeria (Grp B)Mali v Morocco (Grp C)
 • Gabon v Ivory Coast (Grp C)Algeria v Zambia (Grp B)
 • Senegal v Burkina Faso (Grp D)

Labarai masu alaka