Chelsea ta sayi Danny Drinkwater daga Leicester City

Danny Drinkwater Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsohon dan wasan Manchester United din ya ta muhimmiyar rawa yayin da Leicester City ta lashe Premier

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta sayi Danny Drinkwater daga Leicester City a kan fam miliyan 35 gabanin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai ranar Alhamis.

Dan kwallon ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da Leicester City ta lashe kofin Premier a kakar shekarar 2015-16.

Hakazalika Chelsea ta sayi Davide Zappacosta daga kungiyar Torino a kan yarjejeniyar shekara hudu, sai dai ba a bayyana farashin da aka sayi dan wasan ba.

Drinkwataer mai shekara 27 ya yi wa Leicester City wasa 35 a Premier a shekarar da suka lashe gasar.

Labarai masu alaka