Rooney zai gurfana a gaban kotu

Dan wasa Waney Rooney Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rooney shi ne dan wasan da ya fi ci wa Ingila kwallaye a tarihi

Ana tuhumar dan wasan gaban kungiyar Everton Wayne Rooney da yin tuki cikin maye, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

'Yan sanda sun kama dan wasan ne a safiyar ranar Juma'a a garin Wilmslow da ke kasar Ingila.

Dan wasan yana tuki ne bayan ya kwankwadi barasa da ta wuce adaddin da doka ta gindaya, a cewar 'yan sanda.

Sai dai sun ba da belin dan kwallon daga bisani kuma zai bayyana a gaban kotun Majistrin birnin Stockport nan gaba a cikin watan nan.

Rooney ya yi ritaya daga buga wa kasar Ingila wasa a cikin watan jiya.

Dan wasan mai shekara 31 ya koma Everton a bana bayan ya yi shekara 13 a kungiyar Manchester United.

Labarai masu alaka