Man City ce kungiya mai 'yan wasa mafi tsada

Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kyle Walker ya koma Manchester City daga Tottenham kan fam miliyan 45

Wata cibiya mai nazarin kwallon kafa, CIES Observatory ta ce Manchester City kungiyar da take da 'yan wasa masu tsada a tarihi a fagen tamaula.

City ta sayi 'yan kwallo kan fam miliyan 215 a kasuwar da aka rufe a karshen watan nan, hakan ya sa 'yan wasan kungiyar gabaki daya suka kai fam miliyan 775.

Manchester United ce ta uku a jerin kungiyoyin masu tsada, wadda jumullar farashin 'yan wasanta fam miliyan 712. A bara ita ce ta daya, amma ta yo kasa saboda farashin 'yan wasanta da kawai ya karu a bana.

Cibiyar ta CIES ta gudanar da bincikenta ne a Ingila da Faransaa da Jamus da Italiya da kuma Spaniya.

Kungiyoyin Premier shida ne ke cikin goman farko, kuma matsaikacin kulob shi ne mai fam miliyan 287.