World Cup 2018: Za a fara sayar da tikiti a ranar Alhamis

Asalin hoton, Getty Images
Rasha ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta tsayar da ranar Alhamis domin fara sayar da tikitin kallon wasannin gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.
Tuni hukumar ta ce masu sha'awar kallon gasar za su iya neman tikitin a shafinta na Intanet wanda ta shirya sayar wa mataki biyu.
Za kuma ta sayar da shi ne mafi karancin kudi fam 79 a wasannin zagaye na biyu zuwa fam 829 kudin wasan karshe da za a yi a Moscow.
Fifa za ta fara sayar da tikiti a matakin farko tsakanin 16 zuwa 28 ga watan Nuwamba, sannan ta sayar a karo na biyu tsakanin 18 ga watan Afirilu zuwa 15 ga watan Yulin 2018.
Za a fara gasar cin kofin duniya a ranar 14 ga watan Yuni, inda Rasha mai masukin baki za ta buga wasanta a filin Luzhniki da ke Moscow.