Chelsea ta yi kaca-kaca da Qarabag

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea mai rike da kofin Premier ba ta shiga gasar zakarun Turai da aka kammala ba

Chelsea ta fara gasar Zakarun Turai ta bana da kafar dama, bayan da ta casa Qarabag da ci 6-0 a karawar da suka yi a Stamford Bridge a ranar Talata.

Pedro Rodriguez ne ya fara cin kwallo sai Davide Zappacosta ya ci na biyu sannan Cesar Azpilicueta ya kara na uku kafin a je hutu.

Bayan da aka dawo ne Tiemoue Bakayoko da Michy Batshuayi suka ci dai-dai kafin daga karshe Maxim Medvedev ya ci gida.

Daya wasan na rukuni na uku tsakanin AS Roma ta Italiya da Atletico Madrid ta Spaniya tashi suka yi canjaras babu ci.