Marcelo ya tsawaita zamansa a Real Madrid

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid za ta kare kambunta a gasar cin kofin zakarun Turai

Dan wasan tawagar kwallon kafar Brazil, Mercelo ya amince ya tsawaita zamansa a Real Madrid zuwa shekara biyar.

Dan kwallon zai saka hannu a kan yarjejeniyar a ranar Alhamis a dakin taro da manema labarai da ke filin Santiago Bernabeu.

Mercelo ya koma Real Madrid a lokacin da aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a Janairun 2007 daga Fluminense ta Brazil.

Dan kwallon mai tsaron baya ya buga wa Madrid wasa 295 ya kuma ci kwallo 21, ya kuma lashe kofin zakarun Turai uku da na La Liga hudu.

Haka kuma dan kwallon ya lashe kofin European Super Cup biyu da kofin Zakarun nahiyoyin duniya biyu da Spanish Super Cup uku da Copa del Rey biyu.