Real Madrid ta fitar da wadanda za su kara da Apoel

Championleague

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid tana da kofin Zakarun Turai guda 12 a jere

Real Madrid ta bayyana 'yan wasa 19 da za su buga mata gasar cin kofin zakarun Turai da za ta fafata da Apoel Nicosia a ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Madrid ita ce ke rike da kofin da ta lashe biyu a jere kuma na 12 jumulla.

Madrid din ta saka sunan Ronaldo cikin wadan da za su buga mata karawar, bayan da hukumar kwallon Spaniya ta dakatar da shi buga wasa biyar.

Sai dai hukuncin bai shafi na gasar zakarun turai ba, kuma hukumar ta sameshi da laifi a wasan Spanish Super Cup, bayan da ya ture alkalin wasa a fafatawar da suka yi da Barcelona.

Ga 'yan wasan da za su buga karawa da Apoel:

  • Masu tsaron raga: Navas da Casilla da kuma Luca.
  • Masu tsaron baya: Carvajal da Ramos da Varane da Nacho da Marcelo da kuma Theo.
  • Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Isco da Kovacic da kuma Ceballos.
  • Masu cin kwallo: Cristiano Ronaldo da Bale da Lucas Vázquez da Mayoral.