Arsenal za ta buga Europa bayan shekara 20

Europa League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karon farko da Arsenal za ta buga Europa tun bayan shekara 20

Arsenal za ta karbi bakuncin Cologne a wasan cikin rukuni a gasar Europa League a ranar Alhamis, karon farko da za ta buga gasar tun bayan shekara 20.

Tuni kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce zai hutar da manyan 'yan wasansa bakwai da suka hada da Petr Cech da Laurent Koscielny da Alexandre Lacazette da Granit Xhaka da Aaron Ramsey da Danny Welbeck da kuma Mesut Ozil.

A karon farko Jack Wilshere zai buga wa Arsenal wasa, bayan shekara daya, kuma Alexis Sanchez zai buga fafatawar domin ya dawo kan ganiyarsa a tamaula.

Wasu 'yan wasan da za su kara da Cologne sun hada da David Ospina da Shkodran Mustafi da Per Mertesacker da Theo Walcott da kuma Olivier Giroud.

Arsenal za ta buga Europa bayan da ta yi ta biyar a kan teburin gasar Premier da aka kammala, kuma karo na farko da ba ta kare a 'yan hutun farko ba a wasannin bayan shekara 20.