Madrid ta fara kare kambunta da nasara

Asalin hoton, Getty Images
Madrid ta ci kofin Zakarun Turai biyu a jere tana kuma da shi 12 jumulla
Real Madrid mai rike da kofin Zakarun Turai ta fara kare kambunta da kafar dama, bayan da ta ci Apoel Nicosia 3-0 a karawar da suka yi a wasan rukuni na takwas a ranar Laraba.
Real mai kofin zakarun Turai 12 jumulla ta fara cin kwallo ta hannun Cristiano Ronaldo tun kan a je hutu, bayan da aka dawo ne ya kara na biyu a bugun fenariti sannan Sergio Ramos ya ci na uku.
Daya wasan na rukuni na takwas kuwa Tottenham ce ta doke Borussia Dortmund da ci 3-1 a Wembley.
Borussia Dortmund za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu na cikin rukuni, yayin da Apoel Nicosia za ta kece raini da Tottenham a Cyprus.
wasu daga sakamakon wasannin da aka yi:
- Liverpool 2-2 Sevilla
- Feyenoord Rotterdam 0-4 Manchester City
- FC Porto 1-3 Besiktas
- NK Maribor 0-1 Spartak Moscow
- Shakhtar Donetsk 2-1 Napoli
- RB Leipzig 1-1 Monaco