Pogba zai yi jinyar mako shida

Paul Pogba zai yi jinyar mako shida sakamakon raunin da ya yi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Paul Pogba zai yi jinyar mako shida sakamakon raunin da ya yi

Dan kwallon Manchester United Paul Pogba zai yi jinyar mako shida sakamakon raunin da ya yi.

Ranar Talata ne ya yi raunin a wasan cin kofin zakarun Turai da suka kara da Basel, inda suka yi nasar da ci 3-0.

Pogba ba zai buga wasan lig da kulob dinsa zai yi da Everton da Southampton da kuma Crystal Palace ba. kuma ba zai yi wasan zagaye na uku da za su yi ranar larabar makon gobe da Burton ba, da kuma wasan gasar zakarun turai da za su je CSKA Moscow ranar 27 ga watan nan ba.

Haka kuma ba zai shiga wasan neman shiga gasar kofin duniya ta Faransa da za su kara da Bulgaria da Belarus a farkon watan Oktoba ba, wacce suke fatan samun nasara don tabbatar da gurbinsu a Rasha kaka mai zuwa.