An yi wa mai tsaron ragar Burnley tiyata

An yi wa mai tsaron ragar Burnley tiyata a kafada sakamakon raunin da ya yi

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

An yi wa mai tsaron ragar Burnley tiyata a kafada sakamakon raunin da ya yi

An yi wa mai tsaron ragar Burnley Tom Heaton tiyata a kafadarsa, sakamakon raunin da ya yi a wasan da suka kara da Crystal Palace ranar Lahadi, inda suka yi nasara da ci 1-0.

Ben Mee ne ya maye gurbin golan mai shekara 31, bayan da a lokacin da aka samu rabin lokaci a wasan a Turf Moor.

Clarets boss Sean Dyche ya ce, Heaton zai dauki tsawon lokaci kafin ya dawo, domin jinyarsa ta fi karfin makonni

Ya kuma kara da cewa, mun yi farin ciki da aka yi aikin lafiya, amma ba za muyi gaggawar dawo da shi ba, ya kamata ya warke sosai, kuma yana samun sauki.