Isco ya tsawaita zamansa a Real Madrid

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Isco ya lashe kofin Zakarun Turai uku a Real Madrid

Dan wasan Real Madrid, Isco ya amince ya ci gaba da murza-leda a kungiyar zuwa shekara biyar.

Dan wasan tawagar Spaniya mai shekara 25, wanda ya yi wa Madrid wasa 197 ya ci kwallo 34, zai ci gaba da zama har zuwa karshen kakar 2021-2022.

Isco ya lashe kofin Zakarun Turai uku da na La Liga daya da Copa del Rey tun lokacin da ya koma Bernabeu daga Malaga kan fam miliyan 23.

Dan wasan shi ne na biyu da ya tsawaita yarjejeniyarsa da Madrid a makon nan bayan dan kwallon tawagar Brazil, Marcelo.