Aguero ya ci kwallo uku rigis sau shida a Premier

Sergio Aguero ne ya ci kwallo uku rigis a karawar da Manchester City ta doke Watford da ci 6-0 a gasar Premier wasan mako na biyar da suka yi a ranar Asabar.
Bayan da Aguero ya ci kwallo uku a karawar sai Jesus da Otamendi da kuma Sterling wadanda kowanne ya ci daidai a fafatawar.
Wannan ne karo na shida da Aguero ya ci kwallo uku rigis a gasar Premier, kuma Shearer ne ke kan gaba da 11 sai Fowler da tara da Owen da kuma Henry kowanne ya ci sau takwas-takwas.
Wannan ne karo na biyu da Manchester City ta ci kwallo biyar a jere, bayan da ta casa Liverpool a wasan mako na hudu da ci 5-0
City za ta buga wasan gaba da West Brom kafin ta karbi bakuncin Crystal Palace.