Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a La Liga

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona ta ci wasa hudu a gasar La Liga

Barcelona ta doke Getafe da ci 2-1 a wasan mako na hudu a gasar La Liga da suka fafata a ranar Asabar.

Getafe ce ta fara cin kwallo ta hannun Gaku Shibasaki tun kafin a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Barcelona ta farke ta hannun Denis Suarez sannan tsohon dan wasan Tottenham Paulinho ya kara na biyu a raga.

Da wannan sakamakon ya sa Barcelona tana nan a matakin farko a kan teburin La Liga bayan da ta ci wasa hudu a gasar.

Mai rike da kofin Real Madrid za ta ziyarci Real Sociedad a ranar Lahadi, ita kuwa Real ta ci wasa uku da ta yi a gasar ta La Liga.