Damben Dogon Bunza da na Abata Mai

Damben Dogon Bunza da na Abata Mai

Daya daga wasa takwas da aka yi a Safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton

An fara wasan da babu kisa tsakanin Aljanin Sikido daga Arewa Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa

Damben Shagon Jimama daga Kudu da Aminun Mahaukaci Teacher daga Arewa babu kisa a turmi biyun da suka yi

Nokiyar Dogon Sani daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu babu kisa a turmi biyun da suka dambata

Sai Shagon Dan Sama'ila daga Kudu da ya buge Tulan Shagon Tuwo daga Arewa a turmin farko

Dan Matawallen Kwarkwada daga Kudu da Sani Mai kifi daga Arewa turmi biyu suka yi babu wanda ya je kasa.

Garkuwan Isah Kasa daga Kudu da Bahagon Abban Na Bacirawa daga Arewa babu kisa a turmi biyun da suka dambata

Autan Cindo daga Arewa da Autan Faya daga Kudu turmi daya suka yi aka tashi daga wasan