Ousmane Dembele zai yi jinyar wata hudu

Barcelona

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Barcelona ce ta doke Getafe 2-1 a gasar La Liga wasan mako na hudu

Dan wasan da Barcelona ta saya mafi tsada a bana, Ousmane Dembele zai yi jinyar wata hudu.

Dan kwallon da Barca ta sayo daga Borrussia Dortmund kan kudi fam miliyan 135.5 ya yi rauni ne a karawar da Barcelo ta ci Getafe 2-1 a gasar La Liga a ranar Asabar.

A wata sanarwa da Barcelona ta fitar ta ce likitoci a Finland za su yi wa dan wasan na tawagar Faransa aiki a mako mai zuwa, kuma tana sa ran zai yi jinya zuwa wata uku da rabi ko hudu.

Hakan na nufin ba zai buga wa Barcelona wasannin cikin rukuni a gasar cin kofin Zakarun Turai ba, kuma da kyar idan zai kara a fafatawa da Real Madrid a ranar 23 ga watan Disamba.

Dembele ba zai buga wa Faransa wasan shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi da Bulgaria da wanda za ta kara da Belarus a watan Oktoba ba.