Chelsea da Arsenal sun raba maki a Premier

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea tana ta uku a kan teburin Premier, ita kuwa Arsenal tana ta 12

Chelsea da Arsenal sun tashi wasa babu ci 0-0 a gasar Premier wasan mako na biyar da suka kara a ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Chelsea ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da alkalin wasa ya bai wa David Luis jan kati sakamakon ketar da ya yi, watakila ba zai buga wasa uku ba kenan.

Da wannan sakamakon kungiyoyin biyu sun raba maki daidai a tsakaninsu, hakan na nufin Chelsea tana da maki 10, ita kuwa Arsenal tana da bakwai.

Chelsea za ta ziyarci Stoke City a wasan mako na shida a ranar 23 ga watan Satumba, yayin da Arsenal za ta karbi bakuncin West Bromwich Albion a ranar 25 ga watan Satumbar.