Neymar da Cavani na takaddamar buga fenariti

Asalin hoton, Getty Images
PSG ce ta daya a kan teburin Faransa
Kocin Paris St-Germain, Unai Emery ya ce zai shiga tsakanin Neymar da Edison Cavani, idan sun kasa sasanta wa a tsakaninsu kan wanda ya kamata ya buga wa kungiyar fenariti.
'Yan wasan biyu sun yi takaddama kan wanda ya kamata ya buga wa kungiyar fenariti a karawar da PSG ta ci Lyon 2-0.
Daga baya Neymar ya hakura ya bar wa Cavani, inda shi kuma ya buga amma bai ci kwallon ba.
Kocin ya ce ya umarce su da su tsayar da matsaya a tsakaninsu, amma idan ba za su iya ba shi zai yanke hukuncin da ya kamata.
PSG ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburi ne, bayan da ta ci kwallo biyu da 'yan wasan Lyon suka ci gida.