Carvajal ya tsawaita zamansa a Madrid

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid

Bayanan hoto,

Carvahal ya yi wa Real Madri wasa 103 ya kuma ci kwallo biyu

Dan wasan Real Madrid, Dani Carvahal ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da murza-leda a Santiago Bernabeu.

Dan wasan ya saka hannu kan kwantiragin shekara biyar a gaban shugaban Real Madrid, Florentino Perez.

Carvahal mai tsaron baya ya fara wasa a karamar kungiyar Madrid a 2010 daga nan ya koma Bayern Leverkursen a 2012 sannan ya koma Real a 2013, ya kuma buga mata wasa 103 ya ci kwallo biyu.

Ga jerin kofunan da ya lashe a Real Madrid

  • La Liga: 2016-17
  • Copa del Rey: 2013-14
  • Supercopa de España: 2017
  • UEFA Champions League: 2013-14, 2015-16, 2016-17
  • UEFA Super Cup: 2014, 2016, 2017
  • FIFA Club World Cup: 2014, 2016