Barca ta fitar da 'yan wasan da za su kara da Eibar

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 12

Kungiyar kwallon kafa ta Eibar za ta ziyarci Barcelona a wasan mako na biyar a gasar La Liga a ranar Talata.

Kungiyoyin biyu sun kara a kakar bara ta 2016/17, inda Barca ta ci Eibar 4-2 a Nou Camp, sannan ta ci 4-0 a gidan Eibar.

Jumulla sun hadu sau shida a gasar La Liga kuma Barca ce ta lashe dukkan karawar da suka yi, inda ta ci kwallo 20 sannan Eibar ta zura mata uku a raga.

'Yan wasan da za su buga wa Barcelona karawar:

Masu tsaron raga: Marc-André ter Stegen, Jasper Cillessen

Masu tsaron baya: Nelson Semedo, Gerard Piqué, Javier Mascherano, Jordi Alba, Digne, Vidal, Vermaelen.

Masu wasan tsakiya: Ivan Rakitic, Sergio Busquets, Denis Suárez, Andrés Iniesta, Paulinho, Sergi Roberto

Masu cin kwallo: Luis Suárez, Lionel Messi, Gerard Deulofeu