An yi nasarar yi wa Ousmane Dembele aiki

Barcelona

Asalin hoton, Barcelona FC

Bayanan hoto,

Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 12, bayan da ta ci wasa hudu

Likitoci sun yi nasarar yi wa dan wasan da Barcelona ta saya mafi tsada a bana, Ousmane Dembele aiki a ranar Talata.

Dakta Sakari Orava ne ya jagoranci aikin a wani asibiti a birnin Helsinki da ke Finland, kuma likitan Barcelona Dakta Ricard Pruma ke kula da dan kwallon.

Dan wasan mai shekara 20 dan kwallon tawagar Faransa ya koma Spaniya da taka-leda daga Borussia Dortmund a cikin watan Agusta.

Dembele ya yi rauni ne a wasan da Barcelona ta ci Getafe 2-1 a gasar La Liga wasan mako na hudu a ranar Asabar.

Kungiyar ce ta sanar da cewar dan kwallon zai yi jinyar wata uku da rabi zuwa hudu.